Lebanon: Wani Dan Majalisar Dattawan Amurka Ya Ki Amincewa Kan Cewa Hizbullah Ba Yan Ta’adda Ba Ne

Dan majalisar dattawan kasar Amurka Lindsey Graham ya kawo karshen tattaunawarsa da babban kwamandan sojojin kasar Lebanon bayan ya fadi cewa kungiyar Hizbullah a wajen

Dan majalisar dattawan kasar Amurka Lindsey Graham ya kawo karshen tattaunawarsa da babban kwamandan sojojin kasar Lebanon bayan ya fadi cewa kungiyar Hizbullah a wajen mutanen kasar Lebanon ba kungiyar yan ta’adda bane.

Tashar talabijan ta Al-Mayadeetv ta kasar Lebanon ta nakalto Lindsey Graham a jiya Alhamis bayan ya gana da Rodolphe Haykal nay an mintoci a birnin Beirut babban birnin kasar ta Lebanon.

Grahm ya ce: Na tambayi Haikal yaya yake kallon kungiyar hizbullah ta kasarsa? Shin yana daukarta a matsayin kungiyar yan ta’adda sai yana amsa da cewa : ba haka bane a wajen mutanen kasar Lebanon kungiyar Hizbullah ba kungiyar yan ta’adda ba.

Sai Graham ya ce: daga nan kawai ya tashi, don ya san cewa basu da fahinta guda da sojojin kasar ta Lebanon ballatama su tattauna kan yadda zasu yi da ita.

Gwamnatin kasar Amurka dai tana son amfani da sojojin kasar Lebanon don yakar kungiyar Hizbullah wacce ta zama abin damuwa ga HKI wacce take son mamayar kasar Lebanon kamar yadda ta mamaye kasar Syriya, amma ta kasa samun hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted