Rasha : Kasashen Yamma na cikas ga alaka tsakaninmu da Afirka

Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov ya yi Allah wadai da yunkurin kasashen yamma na kawo cikas ga hadin gwiwa tsakanin Moscow da kasashen Afirka.

Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov ya yi Allah wadai da yunkurin kasashen yamma na kawo cikas ga hadin gwiwa tsakanin Moscow da kasashen Afirka.

Mista Lavrov, ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da takwaransa na Chadi Abdoulaye Sabre Fadoul a birrin Moscow, wanda ya ziyarci Rasha da nufin karfafa dangantakar kasashen biyu.  

Ganawar ta  bai wa bangarorin biyu damar sake duba dangantakarsu da kuma ayyana sabbin abubuwan da suka fi muhimmanci.

Ministan Harkokin Wajen Rasha ya sake nanata cewa dangantakar da ke tsakanin Rasha da Chadi ta dogara ne akan “girmama juna, da daidaito.

Tsaro a yankin Sahel da hadin gwiwa da Afirka da Yaki da ta’addanci su ne suka fi mamaye tattaunawar bangarorin biyu kamar yadda shafin RT. Ya rawaito.

Lavrov ya tabbatar da cewa Rasha za ta ci gaba da taimaka wa kasashen Sahel wajen karfafa sojojinsu da kuma horar da su da na tsaro.

A cewarsa, kasashen nahiyar, Ƙungiyar Kasashen Sahel, da Ƙungiyar Tarayyar Afirka, da ECOWAS dole ne su ci gaba da kasancewa manyan masu ruwa da tsaki a harkokin tsaron Afirka.

Ministan na Rasha ya kuma yi Allah wadai da goyon bayan da wasu tsoffin kasashen mulkin mallaka ke bai wa kungiyoyin ‘yan ta’adda domin kawo cikas ga sulhu tsakanin Moscow da kasashen Sahel.

Ganawar ta ministan harkokin wajen Tchadi da na Rasha, na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan ran gadin da Lavrov ya kai a Afrika, inda ya gana da takwarorinsa na kasashen kawancen Sahel AES a Yamai babban binrin Jamhuriyar Nijar inda suka cimma yarjeniyoyi da dama a tsakaninsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted