Kungiyar OIC Za Ta Yi Taro Na Musamman Saboda Abinda “Isra’ila” Ke Yi A Yammacin Kogin Jordan

A wata sanarwa da kungiyar ta kasashen musulmi ta fitar, ta ce a ranar Alhamis mai zuwa za ta yi taron musamman a babbar cibiyarta

A wata sanarwa da kungiyar ta kasashen musulmi ta fitar, ta ce a ranar Alhamis mai zuwa za ta yi taron musamman a babbar cibiyarta dake birnin Jiddah, domin tattauna halin da yammacin kogin Jordan ya shiga da ‘yan mamaye ke sake kwace kasa.

Taron na kungiyar kasashen musulmi din a birnin Jiddah na Saudi Arabia za a yi shi ne a matakin ministocin harkokin waje, saboda yadda “Isra’ila” ta fitar da dokar mayar da kasar yankin yammacin Kogin Jordan da cewa  mallakin gwamnati ne.

Bayanin da kungiyar ta OIC ta fitar ya kunshi yin kira ga kasashe mambobi da su kalubalanci wannan matakin na ‘yan mamaya da suke son gina sabbin matsugunan ‘yan share wuri zauna.

Majalisar tsaron Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi wani zama da ta amince a shigar da kasar yankin yammacin kogin Jordan a matsayin na hukuma. Wannan shi ne karon farko da hakan ta faru, tun a 1967.

Kasashe da dama suna nuna kin amincewa da matakin na Haramtacciyar Kasar Isra’ila wanda yake rusa Shirin kafa wa Falasdinawa gwamnati a karkashin dokokin kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted