Sharuddan da kungiyar ta Hamas ta gindaya tun da fari da kuma take cigaba da riko da su domin kawo karshen yaki su ne; komawar Falasdinawa zuwa gidajensu da aka kore su daga ciki, ficewar sojojin mamaya daga Gaza,sai kuma bari a shigar da kayan agaji tare da sake gina Gaza.
A ranar 25 ga watan nan na Maris ne dai kwamitin tsaro na MDD ya amince da kudurin tsagaita wutar yaki na wani wani dan lokaci, ba kawo karshen yakin baki daya ba.