Rahoto: ‘Yan Gwagwarmaya A Iraqi Ba Za Su Ajiye Makamai Ba

kungiyar gwagwarmaya ta kasar iraqi tace ba za ta amince da batun mika makamanta ba, za ta ci gaba da rike makamanta

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun gwagwarmaya na kasar iraki sun ki amincewa da batun ajiye makamai , kuma sun fayyace cewa ba za su taba mika makamansu ba, adaidai lokacin da gwamnatin kasar take shirin mayar da dukkan makamai karkashin kulawarta

Abdul qadeer al-karbalai mataimakin shugaban bankaren soji na kungiyar Hizbullah ta al nujaba ya fadi aranar  laraba cewa kalmomin kwabe makamai  ko mika makamai ko kuntatawa basu da wuri a yaren kungiyar gwagwarmaya na kasar,

Haka zali yayi tir da rahotanni da kafafan yada labarai suka bayar na canza matsayin kungiyar a siyasar kasar Iraqi, ya jaddada cewa  matakin da ta dauka na ci gaba da kasancewa a wajen, matake na da ya tabbata kuma zai canza ba har abada,

Matakin nuna rashin amincewar yazo ne a daidai lokacin da fira minisatan Iraqi ali al-zaidi yake kokarin bayyana shirye – shiryensa na sanya dukkan makamai su koma karkashin kulawar gwamnati, tun a watan Agustan da ya gabata ne al-zaidi ya umarci jami’an su tsara kudurin doka game da hakan, yayin wani taro da aka gudanar a birnin bagadaza tare da khalid obeidi shugaban kwamitin tsaron kasa na majalisar dokokin kasar iraki

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted