jakadan kasar iran a majalisar dinkin duniya ya aike da wasika zuwa ga babban sakatare janar din majalisar da shugaban kwamitin tsaro ,game da ci gaba da wuce makadi da rawa da amurka take kan kasar iran ta hanyar killacewar da ta yi mata ta ruwa, wanda hakan take dokokin kasa da kasa ne da kuma na majalisar dinkin duniya , kuma tayi tir da mataki kana ta bukaci Amurka da ta girmam dukkan iyakar kasar iran,kuma ta dakatar da killacewar da ta yi mata ta ruwa
Gulam muhsin darzi jakadan iran a majalisar dinkin duniya ya aike da wasikar ce a jiya laraba ga sakatare janar din mdd, Antonio Guttere da kuma shugaban kwamitin tsaro Aglay Balta inda a ciki ta yi tir da matakin da Amurka take dauka na ci gaba da keta hurumin kasar iran da kuma killaceta ta ruwa,
hakazalika jakadan ya bayyana a cikin wasikar cewa iran a shirye take ta mayar da martani kan duk wani matakin wuce gona da iri da amurka take dauka domin hakkinta ne ta kare kanta daga duk wata barazana kuma yayi daidai da kudurin majalisar dinkin duniya mai lamba 51