A Senegal, an fara wani yajin aikin gama-gari na tsawon awanni 72 yau Laraba.
Kungiyar kwadago ta FODT da wsu kungiyoyi goma sha uku a fannin ilimi, lafiya, shari’a, da sufuri ne suka shiga yajin aikin har zuwa Juma’a.
Gwamnati ta bukaci ma’aikata da su yi watsi da yajin aikin, wanda take ganin “ba bisa ka’ida ba ne.”
Bayanai sun ce al’amuran sufurin jama’a sun tsaya cik a Dakar babban birnin kasar.
Tun farkon makon, gwamnati ta dage kan kokarinta na kawo karshen yajin aikin, wanda take ganin “ba bisa ka’ida ba”.
An kuma yi kira ga kungiyoyin kwadago da su nuna kishin kasa a gabanin wasannin Olympics na matasa, wanda za a gudanar a Dakar cikin kwanaki goma.
Kungiyoyin kwadago sun yi Allah wadai da matsin lamba da yunkurin barazana kuma suna kira da a ci gaba da yajin aikin.
Ma’aikatan suna neman a biya su alawus din gidajensu, a sake duba sabuwar Dokar Aiki da kuma daukar matakai kan tsadar rayuwa.