Sojojin Yamen Sun Kai Hari Kan Sojin Saudiya

sojojin kasar yamen sun kai hari kan wajen ajiyar kayayyakin soji filin saukar jiragen sama na kasar saudiya

Dakarun sojan kasar Yamen sun kai hari kan wajen adana kayayyakin soji a bangaren kago a filin hawa da saukar jiragen sama na riyan dake birnin mukalla kuma ta gargadin kasar saudiya game da amfani da kayayyakin fararen hula a aiyukan soji

Kakakin sojin kasar yamen brigediya janara Yahya Saree ya sanar cewa an kai kayayyakin zuwa filin sama ta hanyar  amfani da jiragen sama na saudiya da aka ware don jigilar kayayyaki yace makiya na amfani da filin saukar jiragen sama na riyan wajen tura makamai da sauran kayayyakin soji da nufin yin kisan gilla kan alumar yamen.

A cikin wani bayani na daban da ya fitar  Saree yayi tir da zargin da dakarun hadinguiwa da kasar saudiya ke jagoranta suka fitar  na cewa dakarun sojan yamen sun kaddamar da hare hare kan motoci dake yankin madina da gabashin yankunan dake kasar saudiya , kana ya bayyana zargin a matsayin mara tushe balle madafa, kuma an yi shi ne don bakanta fuskar dakarun sojin kasar yamen a idon duniya

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted