Wani babban Jami’in Sojan Kasar Iran ya fadawa tashar talabijan ta Presstv kan kasar sojojin kasar a shirye suka don yakin fito na fito da makiya ta ko tana ina, a kuma dukkan fagage.
A wata hari ta musamman da tashar talabijan ta Presstv a yau Laraba, Jami’an ya ce, sojojin kasar a shirye suke tsab, don shiga fafatawa da makiya, ta ko ta ina. Kuma na ko wani matsayi ne.
Yace Sojojin Iran a shirye suke su shiga yaki da makiya, kuma zasu lallasasu kamar yanda ya dace idan sun sake yin wani kuskuren. Kuma bararsu a wannan karon ma zai hada da dukkan abinda suka mallaka a yankin da kuma duk abinda mataimaknsu suka mallaka a yankin.
Jami’an ya kara da cewa, akwai zaton cewa, Amurka da HKI ne zasu sake farwa kasar Iran idan hakan ya auku, ba abinda zai raba tsakanin kasashen biyu kan abinda ya shafi Iran.
Daga karshe jami’an ya bayyana cewa, barazanar kasashen biyu ya sa Iran ta kara shiri don fuskantarsu. Wannan kuma saboda kasashen biyu suna fuskantar zabubbuka a cikin makonni masu zuwa.