Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya shawarci Amurka da ta zabi tsakanin cimma yarjejeniya “mai kyau” tare da Tehran, ko kuma ta fuskanci “babban kuskuren dabaru idan ta sake kai wani hari na soja kan Iran.
A cikin wani makala da jaridar Financial Times ta wallafa ranar Laraba, Araghchi ya bayyana cewa dole ne Washington “ta nuna da gaske ta ke yi kuma tana da niyya ta hakika ta kawo karshen hare-harenta har abada.”
“Idan Amurka ta sake zabar amfani da karfin soja maimakon diflomasiyya, ina da tabbacin cewa hakan zai haifar da babbar gazawar dabaru,” in ji shi.
Ya ce Iran, wadda ke da “tsohon tarihi da al’ada mai girma,” ba za ta taba “durkusa wa wani ba,” yana mai jaddada cewa kasar za ta tsaya tsayin daka wajen kare ‘yancin kanta da ikon mallakarta.
Ya sake jaddada cewa Tehran a shirye take ta bi hanyar sulhu cikin lumana, yayin da take da cikakken karfin kare kanta.
Ya kara da cewa, sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, jajirtattu sun koyi darussa masu muhimmanci daga hare-haren da Isra’ila da Amurka tun shekarar 2025.
Araghchi ya yi nuni da hare-haren da aka kai a lokacin da Iran ke tattaunawa da Washington, yana mai tambayar yadda Tehran za ta iya ” sake amincewa da shugaban Amurka.”
“A takaice dai, ba mu da wani amincewa ko kadan kan gaskiyar ikirarin gwamnatin Amurka na cewa tana son zaman lafiya da Iran,” in ji shi.
Ya ambaci hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai a watan Yunin 2025 da Fabrairun 2026, da kuma wani harin a watan Yunin wannan shekarar, wanda ya faru jim kaɗan bayan shugaban Amurka da Shugaban Iran Masoud Pezeshkian sun sanya hannu kan wata yarjejeniya (MoU) da nufin kawo ƙarshen yaƙin.
Duk da waɗannan damuwar, Araghchi ya ce Iran ta ci gaba da nuna aniyarta ta ba wa diflomasiyya wata dama.