Iran: Shugaban Majalisar Dokoki Ya Gana Da Jagora

shugaban majalisar dokokin kasar iran ya gana da jagoran juyin musulunci na kasar iran kuma sun tattauna kan takunkumin tattalin arziki

Mohammad baqeer Qalibaf shugaban majalisar shawarar musulunci ta kasar iran ya gana da jagoran juyin musulunci na iran Ayatullah Sayid Mujtaba Khamena’I inda suka tattauna game da ci gaba da aka samu a baya bayan nan a bangaren soji, da kuma takunkumin tattalin arziki da kasar Amurka ta kakabawa kasar iran

A lokacin ganawar jagoran yayi kira da aka kara karfafa karfin da kasar take da shi kuma yayi ishara game da irin rawar da yan majalisa za su taka wajen kara samar da hadin kan alummar kasar, kuma ya jinjinawa alummar iran game da ci gaba da tarurrukan da suke yi na nuna goyon bayan jamhuriyar musulunci ta iran da kuma jami’an tsaro,

Haka zalika jagoran ya kara yin kira ga gwamanati da majalisa da suyi aiki tare wajen warware matsalolin tattalin arziki da alummar kasa ke fuskanta , da kuma ciyar da  batutuwan da suka shafi abokan mua’mala da alummar kasar gaba

ana sa bangaren shugaban majalisar qalibaf ya yi wa jagoran karin bayani game da matakin da yan majalisar suka dauka tun daga lokacin da Amurka da isra’ila suka kaddamar da yaki kan kasa iran a watan fabareru, da kuma shirin da majalisar ke da shi wajen fuskantar batutuwan da suka shafi kasar da kuma irin  kalu balen da suke fuskanta

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted