Gwamnatin sojin Burkina Faso ta sake dawo da hukuncin kisa, bayan da majalisar dokokin kasar ta amince da sabon kundin hukunta masu laifi, matakin da ya kawo karshen dokar da ta soke hukuncin kisan a shekarar 2018.
Dukkan Mambobin Majalisar Dokokin rikon kwarya ta Burkina Faso su 71 da ba zaben su aka yi ba sun amince da gyara kundin dokar hukunta laifuka da kai tsaye ya dawo da hukuncin kisa da kasar ta Sahel ta yi watsi da shi tun shekarar 2018.
Karkashin sabuwar dokar da ma’aikatar Shari’ar Burkina Fason ta sanar ranar Talata, 20 ga watan Oktoba, ta tanadi hukuncin kisa kan laifuka da suka hada da ta’addanci da leken asiri da cin amanar kasa da kashe mahaifa, da kuma shigo da kayayyakin da wa’adin amfani da su ya kare ko haramtattu, da suke yin sanadin mutuwar wani.
Gwamnatin sojin karkashin kaftin Ibrahim Traore, ta ce matakin zai taimaka wajen tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Sai dai kungiyoyin kare hakkin dan’adam, ciki har da Human Rights Watch da Amnesty International, sun nuna damuwa da dawo da hukuncin kisa, saboda fargabar cewa za a iya amfani da shi wajen murkushe abokan gaba.