Faransa : Kungiyoyi Sun Caccaki Ziyarar Macron A Bahrain

Gwamnatin Al Khalifa, wacce ke kan mulki a Bahrain, ta danne mabiya 'yan Shi'a tsawon shekaru.

A Faransa sama da kungiyoyin kare hakkin dan adam 30 sun yi gargadin cewa ziyarar Shugaban Faransa Emmanuel Macron zuwa Bahrain za ta iya karfafa Manama ta ci gaba da yaki da ‘yan adawa a kasar dake yankin Gulf na Farisa.

A cikin wata wasikar hadin gwiwa da suka aike wa Emmanuel Macron, kungiyoyi 32, ciki har da Cibiyar Kare Hakkin Dan Adam da Dimokuradiyya ta Bahrain (BIRD), Human Rights Watch, da Ƙungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Duniya (FIDH), sun jaddada cewa Bahrain a halin yanzu tana fuskantar mafi munin murkushe ‘yan adawa tun bayan boren jama’a na watan Fabrairun 2011.

Kungiyoyin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sun kuma yi gargadi ga shugaban Faransa, wanda ke neman daddale yarjejeniyoyin makamashi da wasu kasashen Gulf na Farisa, ciki har da Bahrain, inda Suka jaddada cewa karfafa hadin gwiwar siyasa da tsaro zai iya “karfafa hukumomin Bahrain” don ci gaba da murkushe masu adawa.

“Bai kamata Faransa ta sadaukar da hakkin dan adam don cimma yarjejeniyoyi masu riba a Tekun Farisa ba, a karƙashin fakewar tsaron yanki,” in ji Sayed Ahmed Alwadaei, darektan Bankin Duniya.

Gwamnatin Al Khalifa, wacce ke kan mulki a Bahrain, ta danne mabiya ‘yan Shi’a tsawon shekaru.

Don haka hukumomi suna neman dakatar da zanga-zangar goyon bayan dimokuradiyya da ‘yan kasa ke yi.

A ranar Asabar data gabata ne jerin kungiyoyi a faransa suka gugudanar da wata gagarimar zanga zanga tsadar rayuwa da makamashi wacce ta rikice zuwa tarzoma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted