Gwamnatin Somaliya ta yi Allah wadai da taswirar Isra’ila da ke nuna yankinta a matsayin wanda aka raba shi, tana tabbatar da ikonta, hadin kanta da kuma iyakokin da aka amince da su a duniya.
Ma’aikatar Yada Labarai ta Somaliya ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa taswirar da aka gabatar a lokacin wani taron manema labarai da FiraMinistan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi kwanan nan, wanda ya nuna Somaliya a matsayin wacce aka raba ta, mai bayyana hakan da yaudara da karya iyakokin da aka amince da su a duniya.”
Mogadishu ta sake jaddada alkawarinta na ” ga ikonta na kasa, hadin kai da kuma cikakken yankinta kamar yadda “aka tsara a cikin Kundin Tsarin Mulkin Somaliya, Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, da kundin Tsarin Tarayyar Afirka.”