kungiyar Ansarullah Ta Kasar Yamen Tace Zata Mayar Da Martani Kan Harin Da Saudiya Ta Kai Mata

Ofishin siyasa na kungiyar Ansrullah na kasar yamen ya sha alwashin mayar da martani mai tsanani kan harin da kasar saudiya ta kai ma kasar

Ofishin siyasa na kungiyar Ansrullah na kasar yamen ya sha alwashin mayar da martani mai tsanani kan harin da kasar saudiya ta kai ma kasar yamen, kana kuma ta jaddada cewa daga yanzu zata dauki matakin killacewa da killacewa, idan kuma aka zafafa kai mata hari itama za ta zafafa kai hari don haka za ta ci gaba da kai hare-hare kan duk wani har da aka kai mata.

Wannan yana zuwa ne bayan da kasar saudiya ta kaddamar da hari kan kasar yamen a yammacin jiya juma’a akan tashar jirajen ruwa ta hudaid da kuma cibiyar sadarwa ta garin, inda ya samu wani mutum dake aiki a ma’aikatar sadarwar, yar ila yau saudiya ta kai hari a tsibirin kamaran dake garin hudaida  ya samu wata mace guda daya.

Haka zalika ofishin ya kara da cewa lallai kasar saudiya tana kokarin rama gazawar soji da siyasarta ta hanyar kai hari kan muhimman abubuwan rayuwar alummar yamen, yana mai cewa kai harin kan abubuwan more rayuwa na fararen hula  keta hakkin alummar  yamen ne kuma ya sabama dokikin kasa da kasa.

Daga karshe sun jaddada cewa harin da takai a baya bayan nan ba zai tafi haka nan ba ba tare da mayar da martani mai tsanani ba, yace matakin da jagororin kungiyar da alummar kasar za su dauka babu canji kuma a fili yake.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted