210-Assalamu alikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmi na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
////…Madallah, Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma sirar Imam Al-Hassan Al-Mujtaba (s) dan Fatimah (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo mako, a cikin shirimmu da ya gabata mun fara magana dangane da ziyarar Imam Al-Hassan (a) zuwa kasar Sham da kuma munazarorin da ya yi da mu’awiya da mutanensa. Mun kuma bayyana yanda mutanen Sham suka girmama shi, suka yi ta taruwa a wajensa suna sauraron kalamansa da khudubinsa, wanda ya sanya mu’awiya da mutanensa cikin tashin hankali, suka kuma fara tunanin yanda zasu bullo masa (s).
Mun ji yanda Amru dan Asi da Mughira dan Shuba, da Marwan dan hakam, da walid dan ukba da sauransu suka taru a fadar umayyawa a demash, suka fara tattaunawa a tsakaninsu kan yanda zasu bullowa Imam Al-Hassan (a), sannan a lokacinda Mu\awiya ya fito daga gidansa, suka gabatar masa dashawarorinsu kan yanda za’a bullo masa, sai suka bukaci, ya kira shi zuwa fadarsa su kaskantanshi, su zagi mahaifinsa su kuma dora masa laifin kissan Khalifa Uthman, suna ganin ba zai iya kare kansa ba.
Amma Mu’awiya da farko ya ki amincewa da wannan shawarar, saboda ya san ba zasu iya kure Imam Al-Hassan(a) ba, banda haka shi ne zai kunyatasu. Saboda ya jarrabi hakan a lokacinda ya kai ziyarassa ta farko zuwa madina, inda yayi abinda suke son yi, amma a lokacinda Imam Al-Hassan (a) ya mayar masa da martani, sai da yayi nadamar abinda yayi.
Amma wadannan masu kiyayya da banu Hashim kuma masu tsoron Imam Al-Hassan (a) zai iya rusa masu daularsu ta Banu Umayya, sun dage kan cewa sai Mu’awiya ya kira shi don su zazzageshi su kuma wulakanta shi.
Suka kara fada masa cewa : Ka kirashi ya zo mu zage shi mu zagi babansa, mu aibatashi da kissan Uthman, kuma ba zai iya fadar kome ba.
Mu’awiya ya na ganin wawtansu da wannan bukatar, kuma ya san abinda zai faru idan an yi hakan. Amma daga karshe ya amince da bukatar, ya kuma fada masu cewa: Zan ce masa ya bude zuciyarsa ya fadi duk abinda zai fada a kanku.
Sai Mu’awiya ya aikawa Imam Al-Hassan (a) ya zo fadarsa. A lokacinda dan sako ya isa Imam (a) ya ce a bashi rigarsa ta fita waje, ya sanyata, sannan ya fita daga masaukinsa yana karanta wannan addu’ar yana cewa:
{Ya Ubangiji! Ina neman tsarinka daga sharrinsu, ina neman kariya da kai daga sukarsu, ina neman taimakonka a kansu, ka isammani ta yanda kake so, a sanda kake so, tare da karfi da kuma ikonka Ya mafi jinkan masu jinkai}. Ya kama hanya ya zo fadar Mu’awiya.
A lokacinda mu’awiya ya ganshi sai ya tashi da kansa ya tarbeshi, sannan ya fara bashi hakuri yana cewa: ‘Ya baban Mohammad! Wadannan mutane su ne suka aika gareka, suka kuma saba mani,” . Imam (a) ya san abinda yake fad aba gaskiya bane, sai ya amsa masa da cewa:
{Subhanallh! Tsarki ya tabbata ga All…!! Gida gidanka, umurnin shiga gidan yana hannunka, Wallahi da ka amsa bukatarsu da kuma abinda suke bukata a cikin zukatnsu tare da sonka sai ce ka aikata ba dai dai ba, idan kuma sun rijayeka ne kan ra’ayinka ne, sai inda ka nuna rauni, wanne ka yarda wanne kuma baka yarda ba?. Amma da na san su ne, da na aika masu da wanda suke dai dai da su a cikin yayan Abdulmuttalib. Ai ba zaiyu inji tsoronka ko su ba, All..ne mataimaki na, shi ne mai taimakawa salihan bayani}.
Sai Mu’awiya yace: lalle ni bana son kiranka, amma wadan nan sun takura mani kan hakan, …. Mun kiraka don mu tabbatar maka cewa babanka ne ya kashe Uthman, ya kuma zalunce shi, kuma babanka ne ya kashe shi, ka sauraresu ka kuma basu amsa, kada kadaicinka da yawansu ya hanaka amsa masu da duk abinda ka ga dama”.
A lokacinda Mu’awiya ya yi shiru, sai na farkonsu ya fara magana, kuma shi ne Amru dan Asi. Ya fara da zagin Amirul muminina (a) ya tuhumeshi da zagin Abubakar da kin shugabancinsa, tare da cewa yana da hannu a kasan Umar dan Khaddabi, kuma an kashe Uthman tare da zaluntarsa, bai bar wata kalma marasa kyau ba sai da ya dora masa.
Sannan ya juya wajen Imam Al-Hassan (a) yana cewa: Lalle ku Banu Abdul muttalib, bai yuwa All…ya baku mulki, saboda kissan da kuka yiwa Khalifofi da kuma halatta jinanen da All..ya haramta da kuka yi. Da kuma kodayinku na mulki da aikata abinda bai halatta ba.
Sannan kai Hassan (a) kana kodayin khalifanci ya koma wajenka, baka da hankalin na shugabanci ko dabarar hakan. Yaya kagani, yanda All..T ya sonce maka hankalinka, ya bar mafi wawta cikin kuraishawa yana isgili da kai. Yana wawaita ka, saboda mummunan ayyukan babanka.
Abinda ya sa muka kira ka shi ne don mu zageka mu zagi babanka. Amma babanka All..ya isammana shi, Shi kadai. Sannan kai kana cikin hannummu, zamu zabammaka abinda ya dace, kuma da mun kasheka! Da bamu aikata wani laifi wajen All..ba, kuma ba wani mutum wanda zai aibata mu, shin kana iya mayar mana da martani ka karyata mu. ?. Idan kana ganin mun yi karya a cikin wadan nan abubuwan da muka fada, ka bamu amsa. Idan kuma ka kasa, to ka san cewa da kai da babanka azzalumai ne.”.
Ba abinda yake cikin zancensa in banda zagi da zarge zargen ba basa da tushe da kuma kiyayya a fili da ga iyalan gidan manzon All..(s).
Daga nan sai Walidu dan Uqbah ya tashi yana cewa:
“Lalle kun kasance kawunnin Uthman ne, ya kasance da nigari a gareku, sannan ya kuma baku hakkinku, kun kasance surukansa, kuma ya kyauta surukantaka gareku, yana girmamaku, amma kune na farko da yi masa hasada, sai babanka ya kashe shi, ya zalunceshi, ba tare da wata hujja ko uzuri ba, yaya kuka gani a lokacinda All..ya daukan mafa fansar jininsa ya ajiyeku inda kuka dace. Na Rantse da All…lalle su banu Umayya Al-khairi ne ga Banu Hashim, sabanin Banu Hashim garesu, sannan lalle Mu’awiya ya fi ka’. Sai yayi shiru, sai Utbatu dan Abu sufyan (dan uwan Mu’awiya) ya tashi, yana cewa.
‘Ya Hassan! Lalle babanka sharri ne ga kuraishawa a cikinsu, saboda kissansu da yayi, da yanke zumuncin su da yayi, da tsawon takobinda da harshensa, yana kissan rayayye yana kuma zagin matacce, kai kuma kana daga cikin wadanda suka kashe Uthmanu, kuma zamu kasheka saboda haka, … yak u banu Hashin kun kashe Uthman, kuma hakkimmu ne mu kashe ka da dan’uwanka a kan haka, sai dai All..ya isammana a cikin al-amarin babanka, amma kai! Ba mu yi laifi ba idan mun kashe ka kuma bamu yi ta’addanci ba.’
Daga nan Sai Mughira dan Shuba ya tashi, yana cewa: Da farko ya fara da zagin Amirul muminina (a) sannan yace: Wallahi bai aibata shi kan al-amarin kha’inci ba, sai kan kissan uthmanu’ sai ya zauna.
Sai duk suka yi shiru. Daga nan sai Imam Al-Hassan (a) ya tashi, ya bajesu daya bayan daya, yana fidda aibobinsu da kura kuransu, sannan ya bayyana falalar mahaifinsa Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a).
Da farko, ya gabatar da maganarsa ga Mu’awiya dan Abusufyan yana cewa:
{Ya Mu’awiya! Ba wadan nan ne suka zage ni ba, kai ne ka zage ni, laifi wanda ka shirya, da kuma mummunan ra’ayin da aka sanka da shi. Da kuma mummunan halin da ka tabbata a kansa, tsokana da kuma adawa a garemu da kuma ga Mohammad (s) , sai dai ka saurara ya Mu’awiya, ku saurar, wallahi zan fadi magana dangane da kai da su, wanda kadan ne daga cikin munananku, ina gamuku da All..ya ku mutanen nan, shin ko kun san cewa wanda kuka yi ta zaga a yau din nan, yayi sallah ta alkibloli biyu duka, ? alhali a lokacin Ya Mu’awiya kai kafiri ne? kuma ya Mu’awiya ka kafice masu kuma kana ganinsu bata ne, kana bautawa Lata da uzza a cikin batar ka, Na hada ku da All.. ko kun san cewa, shi ne ya yi bai’o’i biyu, ? Bai’ar fatahi da bai’ar Ridhwan, a cikin bai’o’in biyu, ya Mu’awiya kana kafiri a daya daga cikinsu, sannan ka sabawa daya daga cikinsu,
Ina hadaku da All.. ko kun san cewa shi ne mutum na farko da yayi Imani? Lalle kai ya Mu’awiya kai da babanka kuna daga cikin mu’allafatu kulubuhum, ( wato wadanda ake jan ra’ayinsu da kudade don su yi iamani), kuma kai Ya Mu’awiya da mahaifinka, kuna boye kafirci ku bayyana musulunci, ana kodaitar da ku zuwa ga Imani da kudade, na hadaku da All..shin baku san cewa shi ne wanda yake rike da tutan manzon All..(s) a badar ba ? Sannan tutar mushrikai tana hannun Mu’awiya da kuma babansa? Sannan tana tare da shi ya sake haduwa da ku a ranar Uhud da Ahzaba tutar manzon All..(s) tana hannunsa ba ? …}