Kissoshin Rayuwa: Imam Al-Hassan (a) 205

205-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

205-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahari, ko cikin littafin Mathnawi, ko kuma wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///…Madalla, masu sauraro, idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan (s) dan Fatimah (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku, a shirimu da ya gabata, mun tsaya inda muka bayyana cewa Imam Al-Hassan (a) ya koma birnin Madina birnin kakansa kuma mahaifarsa. Sannan cibiyar gwamnatin musulunci na farko. A kan hanyarsa mun ji yadda mutane suke tarbansa suna masa jaje suna kuma tambayansa abinda ya faru, sannan shi kuma ya bayyana masu.

Sannan a lokacinda ya isa Madina mutane sun fito sun tarbeshi, suna masa maraba da dawowa gida. Har’ila yau mun bayyana cewa, bayan komawarsa Madina, babban aikin da ya sa a gaba shi ne karantarwa da kuma tarbiyantar da mutane, mun ambaci dunayen dalibansa wadanda suka zama manya manyan malamai a cikin sahabbai da Tabi’in ko kuma yayansu.

Daga karshe mun yi maganar cewa Imam Al-Hassan (a) ya zama mafka ga musuman da Mu’awiya dan Abusufyan da ma’aikatansa suke zalunta, inda muka bada misali da Sa’id dan Sarh, wanda walin Mu’awiya a Kufa wato Ziyad dan Sumayya ya so ya kashe, sai ya gudu zuwa Madina, yana neman mafaka daga wajensa, kan sharrin Ziyad dan Sumayya, sannan a lokacinda Ziyad ya tabbatar da cewa ya sami mafaka a wajensa, sai ya kama matansa da yayansa da dan’wansa ya tsaresu, daga nan Imam Al-Hassan ya rubuta masa wasika yana bashi umurni kan ya saki mata da yaya da kuma danuwan Sa’id dan Sarh da ya kama ya kuma sake gina masa gidansa da ya rusa, ya kuma dawo masa da dukiyoyinsa da ya kwace.

Amma a lokacinda Ziyad ya karbi wasikar Imam Al-Hassan(s) ya karantata, ya kuma fahinci abinda ke cikinta, ya lura da cewa Imam Al-Hassan (a) bai ambaceshi da cewa shi dan Abusufyan ne ba.

A nane sai Ziyard yayi fushi, ya mayarwa da Imam wata wasikar inda ya bayyana korafinsa kan rashin ambatonsa da dan Abusufyan, kamar yadda Mu’awiya yake son a kira shi, don da cewa yin hakan haramun ne a musulunci. Don shi ba dan Abusufyan ne mahaifiyarsa karuwa ce, a jahiliyya. Don haka ba wanda ya san iyayen yayanta.

Amma sai mu’awiya ya maida shi dan’uwansa saboda yayi masa aiki, sannan shi kuma ziyada yana ganin hakan daukaka shi ne. don haka ya mayarwa Imam Al-Hassan wasika, yana cewa:

Daga Ziyad dan Abusufyan zuwa ga Al-Hassan dan Fatimah. Bayan haka: wasikarka ta zo mani inda ka fara ambaton kanka kafin ka ambace ni, kai ne kake da bukata a gareni ni sarki ne, matsayinka kamar sauran mutanene, amma ka rubuta kana umurtata kamar kai mai iko ne a kaina, kuma ka rubuta mani kana neman ceton fasiki wanda ya fake da kai. Saboda mummunan ra’ayinka, shi kuma ya yarda da kai kan hakan,

Na rantse da All..ba zai kubuce mani ba, ko da ya shiga tsakanin fata da tsokar jikinka…..ka mika shi da zuwa ga wanda ya fi cancanta da kai, kan abinda ya aikata, ko na yi masa afwa ba don na amince da cetonka gareshi bane, idan kuma na kashe shi, na kasheshi don sonda ga babanka fasiki, wassalam.

A wannan wasikar Ziyad ya bayyana hakikanin daudarsa, da muninsa. Ya nuna rashin kunyarsa, da kuma rashin godiyarsa ga wadanda suka rikeshi suka daukaka shi a baya, ya manta da ni’imomin da Amirulmuminina (a) yayi masa a baya, haka ma wadanda dansa Imam Al-Hassan (a) yayi masa, a lokacinda suka bashi gwamna ko shugabancin wani bangare na kasar Farisa a lokacinda suke da iko da shi.

Amma a halin yanzu, ya musaya al-khairin da suka yi masa da mummuna. Ya kaficewa ni’imar da suka yi masa.

Abin mamaki, shi an yi zamaninda, mutum kamar Ziyad wanda mahaifiyarsa mai tuta ce a jahiliyya, yake zagin wasiyan Manzon All..(s) ya wulakantasu?

Ba abinda ya sa shi yin haka sai don dan ikon da ya samu, na kwana biyu.

In ba don wannan ba, wani martaba ko matsayin da dan sumayya yake da shi da za isa shi ya wulakanta jikin Manzon All..(s) ya sauke matsayinsu. ?

A lokacinda wasikar Ziyad ta shiga hannun Imam Al-Hassan (a) ya karantata, sai ya yi murmushi. Saboda ya san abinda ya sa ya mayar masa amsar wasikarsa da wannan zafin. Imam (a) ya san cewa yayi haka ne don yaki nasabta shi ga Abusufyan ne.

Daga nan sai Imam Al-Hassan (a) ya tashi ya rubuta wasika ga Mu’awiya dan Abu sufyan, ya bayyana masa abinda ya faru, ya kuma masa da wasikar da Ziyad dan Sumayya ya rubuta masa, a cikin wasikar.

Sannan ya sake rubuta wata wasikar ya mayarwa Ziyad dan Sumayya, kan wulakanta shi da kuma mahaifin (s) da yayi. Sannan ya bayyana masa matsayinsa na gaskiya, ya musanta dangantakarsa da Abusfyan, mun karanta wasikar a cikin shirye shiryemmu na baya, ba zamu maimaita ba.

A lokacinda wasikar Imam (a) ta isa ga Mu’awiya, ya karantata, ya kuma karanta irin abinda Ziyad ya fadawa Imam (a) a cikin mummunan wasikarsa, yayi mamakin irin jur’an da Ziyad ya nuna, a cikin abinda ya fadawa Imam Al-Hassan(a).

Sai yayi sauri ya rubutawa Ziyad wasika inda yake aibata shi da abinda ya fadawa Imam Al-Hassan(a) a cikin wasikar sa. Ga kuma nassin wasikar da Mu’awiya ya aikawa Ziyad, bayan ya karanta wasikar Imam (a):

Bayan haka, lalle Hassan dan Ali (a) ya aika mani wasikarka gareshi, wanda jawabi ne ga wacce ya rubuta maka dangane Sa’id dan Sarh.  

Na yi mamakinka, Ya Ziyad, na kuma kara mamakinka!!!. Kuma kasan cewa kana da al-amura biyu dangane da iyayenka, daya na Abusufyan, dayan kuma na Sumayya, amma na bangaren Abusufyan mafarki ne da fata, ammam na sumayya babu wanda ya fishi, shi ne hakika.

Amma mamakina na biyu shi ne, ta yaya zaka rubuta wasika ga Al-Hassan (a) ya zagi mahaifinsa, ka ce masa shi faiski ne? Na rantse da All..kai kafi zama fasiki kan babansa. Sannan kana cewa Al-Hassan(a) ya fara da kansa kafin ya ambaceka, wannan ba zai kaskanta ka ba da ka hankalta, Amma dangane da ikonsa a kanka, ai hakkinsa ne, mutum kamar Al-Hassan ya salladu a kanka, ya umurce ka.

Amma dangane da kinka, na bashi ceto ga wanda ya nemi cetonsa daga wajenka, wajenka, rabo ne a gareka, sai ka ki karbansa, ( wato mutum kamar Al-Hassan(a) ne zai nemi wani abu a wajenka, sai ka ki amincewa, kai ne ka yi asara), ka yi asaran biyan bukatar wanda ya fika cancanta a kan kome.

Don haka, idan wasikata wannan ta zo maka, ka saki duk abinda yake hannunka na dukiyar Sa’id dan Sarh, ka sake gina masa gikinta, ka mayar masa da dukiyarsa, kada ka sake tanka masa. Kuma na rubutawa Al-Hassan (a) da ya bashi zabi nay a zauna a wajensa ko ya koma kasarsa. Daga yanzu baka da iko a kansa, kada ka taba shi, ko ka zageshi.

Amma dangane da abinda ka rubutawa Al-Hassan (a), ka danganta shi da mahaifiyarsa ka ki ka ambaci mahaifinsa,  kaitonka ka san wacece mahaifiyarsa kuwa, ? shin baka san cewa yafi son a dangantashi da mahaifinsa ba kan mahaifinsa. Shin baka san cewa mahaifiyarsa Fatima diyar Manzon All..(s) ba ne.?. wannan ya fi zama abin alfakhari gareshi kan kan danganta shi da mahaifinsa, inda ka sani kuma kana da hankali.

Dana nan sai Mu’awiya ya rubuta wata kasida a karshen wasikar yana yabon Imam Al-Hassan (a). yana cewa:

Amma Hassan(a) shi da ne ga wanda ya zo gabaninsa.* Idan ya tafi, mutuwa tana tafiya ta inda ya tafi.

Shin kana tsammanin Zaki ya Haifa, in ba irinsa ba?  To, wannan Hassan mai kama da shi ne irinsa.

Sai dai da za’a kwantanta hakuri da hankali* Da sunce, kamar dutsen Yuzbalu ne da dutsen Thabil.

A cikin wannan qasidar Mu’awiya ya tabbatar da matsayin Imam Al-Hassan a cikin musulmi, yace, da an kwatanta hakurinsa da duten Thabil da ke tsakanin Makka da Mina da hukurin Imam Al-Hassan (a) ya rinjayi dutsen Thabil, saboda nauyin hakurinsa.

Kaiton zamani, wanda ya kawo wani mutum kamar Ziyad wai yana son kaskanta jikan Manzon All..(s), ya zahe shi ya zagi iyayensa(s).

A wannan al-amarin muna iya fahintar cewa, Mu’awiya dan Abu sufyan, ya san wani bangare na matsayin da All..Ta’ala ya bawa iyakan gidan Manzon All..(s) don yi ji ko kuma ya ga yanda Manzon Allah (s) yake girmamasu yake kuma bayyana matsayinsu. Don haka cutar da su da yayi, bisa bisira yake yi, saboda ba abinda ya boyu gareshi na cancantarsu da shugabanci da kuma matsayinsu a cikin al-ummar musulmi.

Amma wawaye kamar Ziyad dan Sumayya duk tare da cewa, ya yi aiki wa Imam Aliyu (a) na wani lokaci, hakama Imam Al-Hassan (a), amma ya kasa fahintarsu. Na taba jin cewa Imam Ali (a) ya taba fada masa cewa, kasancewarsa dan karuwa a jahiliyya ba zai cutar da shi ba, idan ya ji tsoron All..ta, don haka kada ya ji kome, yayi aiki don samun yardarm All.., ammam da alamun bai ji nasihar limaman zamaninsa kuma wasiyin Manzon All..(s). son duniya ya debeshi ha rya kaiga yana fasikantar da Imam (a). inna lillah wa inna ilaihi rajiun.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alaikum wa rahamatullaji wa barakatuhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted