Babban Sakatare Janar na Kungiyar gwagwarmaya ta Asaib Ahl al-Haq a Iraki, Sheikh Qais Khazali, ya bayyana cewa shahadar babban sakataren kungiyar Hizbullah, babban jigo Sayyed Hassan Nasrallah, “ba za ta tafi haka nan, kuma za ta share hanyar isa zuwa ga bababr nasar.
A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Al Mayadeen, wanda aka gudanar a gefen taron tunawa da shahadar Sayyid Nasrallah da aka yi a birnin Tehran a ranar Juma’a, al-Khazali ya ce: “Muna tare da dukkanin mayakan gwagwarmaya da zalunci a duniya, musamman mu a Iraki, muna da hadin kai tare da ’yan’uwanmu a Lebanon har sai an samu gagarumar nasara”.
Har ila yau ya yi ishara da ci gaban da yankin ke fuskanta bayan shahadar kwamandan dakarun Quds na dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) Qasem Soleimani, inda ya ce tuni aka fara samun sakamako.
Haka nan ya kara jaddada matsayarsu dangane day akin kare dangi na Haramtacciyar kasar Isra’ila a Gaza, inda yace suna tare da Gaza, kuma zasu ci gaba da gwagwarmaya har sai an kawo karshen kisan kiyashin Isra’ila a kan al’ummar gaza.