A wani bangare na ci gaba da karfafa alakar abota, hadin kai, da hadin gwiwa tsakanin kungiyar Kasashen Sahel (AES) da Tarayyar Rasha, an gudanar da zaman tattaunawa na biyu tsakanin Ministocin Harkokin Waje na Ƙungiyar da Tarayyar Rasha a Niamey.
A karshen taron bangarorin sun fitar da sanarwa kamar haka :
Duk bangarorin biyu sun yi maraba da ingancin tattaunawar siyasa tsakaninsu, da kuma ci gaban da aka samu wajen aiwatar da matakan da suka biyo bayan zaman tattaunawa na farko tsakanin Ministocin Harkokin Waje.
Dukan bangarorin biyu sun amince su ci gaba da haɗin kai, goyon bayan juna, da hadin kai a Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran kungiyoyi da hukumomi na duniya.
Sun kuma bayyana niyyarsu ta kara hulda don gina tsarin duniya mai adalci da kuma yaki da mulkin mallaka na zamani.
Duk bangarorin biyu sun yi maraba da kyakkyawan ci gaban tattaunawar da aka yi tsakanin ƙasashe membobin Ƙungiyar AES da ECOWAS da Tarayyar Afirka.
Duk ɓangarorin biyu sun yi maraba da ƙarfafa haɗin gwiwar soja da fasaha tsakanin ƙasashe membobin Ƙungiyar AES.
Duk ɓangarorin biyu sun yi Allah wadai da hare-haren ta’addanci da suka faru a kasashen na Ƙungiyar AES. Sun kuma yaba da gagarumin gudummawar da Rundunar Sojojin Rasha ke bayarwa wajen yaƙi da ta’addanci da rashin tsaro a yankin Sahel.