Mataimakin minstan harkokin wajen Iran Kazim Garib Abadi ya bayyana cewa; Donald Trump ba ya fahimtar wani harshe sai na karfi.
Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya wallafa sako a shafinsa n asada zumunta da yake cewa: Maganganun da Trump ya yi ba suna nuni ne da karfi ba, suna nuni ne da cin kasa akan siyasar kasarsa na tsawon shekaru mai cike da takura da matsin lamba da takukunkumai amma ba su iya tilasta al’ummar Iran ta mika wuya ba.
Garib Abadi ya ci gaba da cewa abinda ya zama wajibi a aikata shi ne yin Magana da Donald Trump mai laifi, kuma makashin kananan yara da harshen da yake fahimta fiye da kowane iri da shi ne karfi.