Wani babban jami’I a kungiyar Ansarullah ta kasar Yamen ya bayyana cewa zanga-zangar da aka gudanar ta jana’izar jagoran juyin musuluni na kasar iran Ayatullah shahid imam khamanai a kasar yamen ta kasance tamakar kuri’ar raba gardama ce kan tsarin siyasar iran da kuma tsayin daka, ya kara jaddada cewa kasashen musulmi suna ci gaba da hada kai don nuna goyon baya ga alummar falasdinu wajen fuskantar manyan kasashe ma’abota girman kai .
Mahbashi wanda yake mamba ne a bangaren siyasa na kungiyar Ansarullah yace kashe jagoran juyin musulunci na iran da Amurka da Isra’ila suka yi yana daga cikin ta’addanci na kasa da kasa, kuma yana cikin ayyukan keta duk wata yarjejeniya da kaidojin dan adamtaka.
Hala zalika yace ya lura wasu kasashe masu rauni a yankin babban abin da ya fi damunsu shi ne cika cikinsu kawai, sun zama kamar shanu da Amurka take tatsa ,a daidai lokacin da kasashen da jagororinsu malamai ne dake da dangantaka mai karfi da alqurani mai girma ba za su taba sassautowa kan hakkokinsu ba, kuma ba za su mikawa wuya ba ko mi runtsi ko tsanani.
daga karshe yace kasar iran ta kara zama mafi karfi bayan yakin baya bayan nan da ta yi da Amurka da Isra’ila , kuma karfinta bai takaita ga jirage masara matuki da makami mai linzami ko shirin nukiliya ba kawai ya dogara ne da karfin Allah da kuma tsayin Dakar alummarta. yace kasar iran hizbullah da Ansarulla da dukkan kungiyoyin gwagwarmya a yankin baki daya sun sha alwashin yantar da yankin falasdinu da aka mamaye