Dakarun Kare Juyin Musulunci Na Iran Sun Kai Harin Ramuwar Gayya A Kasashen Bahrain Da Kuwait

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun kare juyin musulunci na kasar Iran sun kaddamar da hare hare kan muhimman wurare a sansanin sojin Amurka dake kasashen

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun kare juyin musulunci na kasar Iran sun kaddamar da hare hare kan muhimman wurare a sansanin sojin Amurka dake kasashen baharain da kuwaita a matsayin martani kan hare-haren baya bayan nan da  Amurka ta kawo a sassa daban daban a kasar iran

A cikin wani bayani da dakarun suka fitar a yau Alhamis sun nuna cewa hare-haren da suka kai sun fada akan sansanin sojin Amurka dake Arfijan da kuma Ali salim dake kasar kuwaita sai  kuma shaikh isa dake baharain, kuma harin na jiragen sama marasa matuki da makamai masu linzami sun fada kan inda aka harba su

Wadannan bayanai suna zuwa ne bayan da jiragen yakin Amurka suka kaddamar da hare-hare a kan muhimman wurare na amfanin jama’a a kudacin kasar iran ,kuma yayi sanadiyar mutuwar mutum guda ,kuma sun kai hari kan gadoji a arewacin lardin Golestan

Har ila yau dakarun kare juyin  musulunci na iran sun jaddada cewa babban abin da ya kara turnuka zuciyan Amurka ta hasala shi ne irin yadda miliyoyin mutane suka fito kwansu da kwarkwatarsu musamman a kasar iraki  wajen jana’izar jagoran juyin musulunci na kasar Shahid Ayatullah sayyid Ali khamana’i.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted