Gwamnonin arewacin Najeriya hadi da shugabannin gargajiya sun bayyana goyan baya ga shirin samar da ƴan sandan jihohi a kasar, suna masu jaddada bukatar magance matsalolin da ke haddasa rashin tsaro tun daga tushe.
Shugabannin na arewa sun ce za su ci gaba da rubanya kokarinsu na kawo karshen matsalar tsaro, ta hanyar karfafa hadin gwiwa tare da bai wa jami’an tsaron tarayya hadin kai a kokarin da suke yi.
Matakin ya biyo bayan taron da suka gudanar a jiya laraba a dakin taron Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna, inda suka yi nazari game da halin da tsaron yankin ke ciki tare da bukatar a dauki matakan gaggawa.
Ƙungiyar ta bayyana kwarin gwiwar da take da shi ga sabon kwamitin amintattu na shirin tallafin tsaro na arewacin Najeriya, wanda jihohi mambobi za su rika bayar naira biliyan 1 duk wata don karfafa tsaron yankin.
Ƙungiyar ta sha alwashin magance talauci, da rashin aikin yi, da rashin ilimi, da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta, wadanda ta ce su ne manyan abubuwan da ke haddasa matsalar tsaro a Arewacin kasar.