Dazu da hantsi na lokacin Iran ne jirgin sama mai dauke da gawar jagora shahidi da iyalansa ya sauka a filin jiragen sama na Shahid Hashimi Najad domin kai ta hubbaren Imam Ridha da za a yi jana’iza da karshe da binne shi acan.
An kawo gawar jagora shahidi da ta iyalansa da su ka yi shahada a tare da shi ne daga kasar Iraki, bayan da aka kai su birnin Najaf na Imam Ali ( a.s) da kuma Karbala din Imam Hussain ( a.s).
Miliyoyin mutanen kasar Iraki da sun kai miliyan 7 ne su ka yi bankwana da gawar jagora shahidin da kuma iyalansa a cikin biranen na Najaf da kuma Karbala.
Cincirindon mutane a birnin Karbala ya sa an yi jinkirin dawo da gawar shahidin zuwa Iran, saboda har kusan karfe 2;00 mutane suna ci gaba da kwarara kan tituna ba tare da kakautawa ba.
Tun a ranar Juma’ar da ta gabata ne dai aka fara gudanar da jana’izar jagoran anan birnin Tehran, da wakilan kasashe mabanbanta su ka yi bankwana da shi. Fiye da kasashe 100 ne na duniya su ka aike da wakilansu zuwa wurin jana’izar.
A ranakun Asabar da Lahadi kuwa an ajiye gawar jagora shahidin a babban masallacin Tehran inda al’ummar kasar su ka rika cincirindo domin yin bankwana da shi har zuwa ranar Lahadi.
Daga nan ne kuma aka kai gawar jagora shadinin zuwa birnin Qum, a masallacin Jamkaran daga can kuma zuwa hubbaren Fatimah Ma’asuma ( a.s).
A yau Alhamis ne kuma za a binne jagora shahidin a hubbaren Imam Ridha ( a.s) dake birnin Mashhad.