An yi jana’izar karshe wa shahid Ayatollah Khamenei a Mashhad

A Mashhad Miliyoyin mutane ne suka isa a hubbaren Imam Reza (AS) da ke birnin domin yin bankwanan karshe ga Jagoran juyin juya halin Musulunci

A Mashhad Miliyoyin mutane ne suka isa a hubbaren Imam Reza (AS) da ke birnin domin yin bankwanan karshe ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatollah Seyyed Ali Khamenei kafin a binne shi.

Tunda farko dai Jirgin sama dauke da gawar shahidin da iyalansa ya isa a filin jirgin saman Shahid Hasheminejad da ke Mashhad, kafin a fara jana’izar ta karshe da kuma binne shi.

Bayanai sun ce an jana’izar da dan jinkiri sakamakon yawan masu makoki a Iraki, inda miliyoyin mutane suka halarci tarurukan bankwana a biranen Najaf da Karbala masu tsarki.

Kwamitin da ke kula da shirya tarurukan ya bayyana cewa, saboda kyakkyawar tarba da al’ummar Iraki suka yi masa, an sake tsara jana’izar daga karfe 8:00 na safe zuwa karfe 2:00 na rana (agogon gida) a ranar Alhamis.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi shahada, tare da wasu daga cikin iyalansa, a ranar 28 ga Fabrairu, ranar farko ta yakin zalunci da Amurka da gwamnatin Isra’ila suka shelanta wa Iran.

Jana’izar, wadda ta dauki tsawon kwanaki da dama, ta fara ne a ranar Juma’a a Babban Masallacin Imam Khomeini da ke Tehran, inda manyan baki da malaman addini na kasashen waje suka yi masa ban kwana.

A ranar Litinin, miliyoyin ‘yan Iran sun cika titunan Tehran don don ban kwanan karshe, kafin a ci gaba da gudanar da bukukuwan a ranar Talata a birnin Qom mai tsarki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted