Kalibaf: Ba Za A Bude Mashigar Hurmuz Ba Sai Akan Yadda Iran Ta Tsara

Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf ya gargadi Amurka akan ci gaba da kai wa Iran, yana mai cewa duk wani hari,

Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf ya gargadi Amurka akan ci gaba da kai wa Iran, yana mai cewa duk wani hari, zai fuskanci mayar da martani.

Muhammad Kalibaf ya kuma ce har yanzu Amurka ba ta koyi darasi akan cewa duk nuna halayyar daba, da karya alkawali ba za su wuce haka siddan ba tare da biyan farashi ba.

Bugu da Kari Kalibaf ya ce: Bari in yi Magana da ku da gwari-gwari. Duk wani hari da za ku kawo, to kuma za a mayar muku da kwaryar biki, don haka kar ku kidimar da kanku, domin za ku kara nutsewa ne a cikin tabo.”

Haka nan kuma ya ci gaba da cewa, babu yadda za a bude mashigar Hurmuz bisa barazanar Amurka, said ai bisa yadda Iran ta tsara.

Shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran dai ya bayyana hakan ne bayan hare-haren mayar da martani da Iran ta yi akan sansanonin Amurka a safiyar yau Alhamis.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted