Kasashen Equatorial  Guinea Da Gabon Sun Warware Sabanin Kan Iyakokinsu Na Tsawon Shekaru 50

Wadanda su ka wakilci kasashensu wajen rattaba hannun su ne ministan harkokin wajen Equatorial Guinea Simeon Oyono Esono Angue, sai kuma shugaban kotun tsarin Mulki
taswiarar iyakokin kasashen Afirka

Kasashe Gabon da Equatorial Guinea sun rattaba hannu akan yarjejeniyar da ta kawo karshen sabanin da suke da shi akan wasu kananan tsibirai guda uku a yankin da yake da albarkantun man fetur.

Rattaba hannu akan yarjejeniyar wanda aka yi shi bayan da kotun duniya ta yanke hukunci akan mika yankin ga Balabo da hakan ya kawo karshen rikicin da ya dauki shekaru 50 ana yinsa.

Tun a cikin shekarun 1070’s ne kasashen biyu suke jayayya akan wanda yake da hakkin mallakar tsibirin Mbanie da   girmansa bai wuce Hekta 30 ba, sai kuma wasu kanana da su ne cocotiers da Conga.

Tsibiru da ake da sabani akansu kanana ne, kuma babu mutanen da suke rayuwa a  cikinsu, said ai suna a cikin wani yanki ne mai cike da albarkatun man fetur.

A cikin watan Mayu na shekarar 2025 ne dai kotun Majalisar Dinkin Duniya ( ICJ) ta yanke hukunci akan tsibirun tare da mika su ga kasar Equatorial Guinea.

Kasashen biyu dai sun rattaba hannu ne akan amincewa da hukuncin na kotun duniya a wani kwarya-kwaryar biki da aka yi a babbar shalkwatar kungiyar Tarayyar Afirka ( AU) dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Wadanda su ka wakilci kasashensu wajen rattaba hannun su ne ministan harkokin wajen  Equatorial Guinea Simeon Oyono Esono Angue, sai kuma shugaban kotun tsarin Mulki na kasar Gabon, Dieudonne Aba’a Owono

Shugaban cibiyar tarayyar Afirka Muhammad Ali Yusu ya yi  maraba da kawo karshen rikicin iyakoki a tsakanin kasashen biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted