Kasar Turkiyya Ta Yi Barazanar Shiga Tsakani A Yakin Da Yahudawa Suke Yi Gaza

Shugaban kasar Turkiyya ya bayyana cewa: Kasarsa a shirye take ta tsoma baki kan abubuwan da haramtacciyar kasar Isra’ila take aikatawa kamar yadda ta yi

Shugaban kasar Turkiyya ya bayyana cewa: Kasarsa a shirye take ta tsoma baki kan abubuwan da haramtacciyar kasar Isra’ila take aikatawa kamar yadda ta yi a Karabakh da Libya

Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya yi gargadin cewa: Turkiyya na iya shiga tsakani kan ayyukan wuce gona da iri da haramtacciyar kasar Isra’ila ke aikatwa a Falasdinu, don dakatar da yakin da take yi a Zirin Gaza, kamar yadda ta shiga tsakani a rikicin Armeniya da Azarbaijan kan yankin Karabakh, sannan kuma ta shiga tsakani a rikicin kasar Libiya.

A jawabin da ya gabatar a zaman taron jam’iyyarsa ta (Adalci da Ci gaba) a jihar Rize, Erdogan ya bayyana cewa: Kamar yadda kasarsa ta shiga tsakani a rikice-rikicen Karabakh da Libya, a halin yanzu ma zata iya yin haka a yakin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila take yi kan Gaza, kuma babu dalilin da zai hana yin hakan.

A farkon wannan watan nan ne ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila Yisrael Katz ya zargi shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan da bayar da tallafin kudi da makamai ga kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, domin yakar yahudawan sahayoniyya.

Share

3 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments