Rahotanni sun bayyana cewa kasar Saudiya ta bukaci a shiga tsakaninta da gwamnatin kasar Yamen dake da hedkwata a birnin sana’a a daidai lokacin da wani sabon rikici ke neman barkewa tsakanin bangarorin guda biyu
Kamar yadda Jaridar larabci ta Al-akhabar ta kasar labanon ta tsaigumta gwamnatin saudiya ta dauki matakin neman bangaren kasa da kasa da na yankin su shiga tsakani kan batun da ya shafi kasar Yamen bayan hari da aka kai kan filin saukar jiragen sama na Sana’a da kuma martani da kasar yamen ta mayar da hakan ya haifar da fargabar barkewar wani sabin rikici tsakaninsu
Jami’an gwamnatin yamen dake birnin Sana’a sun kara gargadin kamfanoni sufurin jiragen sama da su guji zirga-zirga a sararin samaniyar kasar saudiya, domin za su ci gaba da kaddamar da hare-hare har sai an janye takunkumin da aka sanyawa filin saukar jiragen sama na birnin sana’a.
A martani da kasar saudiya ta mayar ta fara shirye shiryen ganin an yi sulhu inda Qatar da oman za su shiga tsakanin don yayyafama wutar ruwa, majiyoyin siyasa na kasar saudiya sun sanar wa da masu shiga tsakanin cewa ba tada alhakin harin da aka kai a yan kwanakin nan a filin saukar jiragen sama na saan’a, kuma ta dora alhakin hakan kan gwamnatin yamen dake Adan dake kawance da birnin Riyadh.