Hukumomin a saliyo sun dukkufa wajen ci gaba da shirye shiryen karbar bakucin tawagogi daga kasashen yammacin Afrika da za su halarci taron ECOWAS karo na 69.
A ranar lahadi 19 ga watan Yuli ne Shugabanin kasashen yankin za su hadu a Saliyo, kuma wannan shi ne karon farko da kasar za ta karbi bakuncin irin wannan taron na ECOWAS.
A kokarin da hukumomi a Saliyo ke yi na shirya wannan taro, ƴan adawa sun bayyana fatan ganin an yi taron a Lungi, duk da haka,’ƴan adawa sun yi imanin cewa za a iya gudanar da taron a babban birnin, inda kayayyakin more rayuwa suka riga suka wanzu.
Idrissa Mamoud Tarawallie wani mai bincike, yace irin wanan taro mai ya gudana a shekarar 1980, babban taron kungiyar hadin kan Afirka ,kungiyar da ta zama tarayyar Afirka (AU),da dama daga cikin ƴan kasar na tuni da haka, tun bayan wannan taro, kasar ta kasa murmurewa daga matsin tattalin arziki da ta shiga tun bayan taron na AU.