Kasar Lebanon tana ci gaba da fuskantar hare-haren wuce gona da iri, inda aka samu karin shahidai da dama da raunuka a Beka’a da Ain al-Hilweh
Akalla ‘yan Lebanon 10, ciki har da iyali guda ɗaya, suka mutu, wasu 50 kuma suka jikkata a wani harin wuce gona da iri da jiragen saman yakin sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan gine-ginen zama a kwarin Beka’a da ke gabashin Lebanon.
Wani jirgin sama mara matuki ciki na sojojin mamayar Isra’ila ya kai hari kan sansanin ‘yan gudun hijira na Falasdinawa na Ain al-Hilweh da ke kudancin Lebanon, inda ya yi sanadiyar shahadan mutane biyu tare da raunata akalla wasu uku na daban.
Harin ya yi barna mai yawa ga gidajen mutane da kayayyakin more rayuwa na fararen hula a sansanin. Ma’aikatan ceto da na kashe gobara sun yi gaggawar zuwa wurin da abin ya faru don ba da taimako ga wadanda abin ya shafa da kuma jigilar wadanda suka jikkata zuwa asibitoci da ke kusa don neman magani.