Ofishin jakadancin Iraki a Amurka ya tabbatar da cewa: Iraki kasa ce mai cin gashin kanta kuma tana da hakkin kulla yarjejeniyoyin da kuma yarjejeniyar fahimtar juna. An yi nuni da cewa, yarjejeniyar tsaro da aka rattabawa hannu a baya-bayan nan tsakanin Iran da Iraki ta zo ne a cikin tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu don tabbatar da tsaro da kuma kula da kan iyakokin kasashen biyu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa: Ofishin jakadancin ya bayyana a cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labaran kasar Iraki INA ya watsa cewa: “A matsayin martani ga kalaman da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi a yayin taronta na ‘yan jarida na baya-bayan nan, Iraki kasa ce mai cikakken ‘yancin kai, kuma tana da hakkin kulla yarjejeniyoyin da kuma bayanan fahimtar juna bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkinta da dokokin kasa, kuma ta hanyar da ta dace da manyan muradunta.”
Ta kara da cewa, “Iraki na jin dadin huldar sada zumunci da hadin gwiwa da kasashe da dama a duniya, ciki har da kasashe makwabta, Amurka, da sauran kasashe abokantaka, kuma tana da sha’awar gina wannan dangantakar bisa tushen mutunta juna da moriyar juna.”