Iran : Jagora ya gode wa jama’a kan halartar tarurukan jana’iza  

Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatollah Seyyed Mojtaba Khamenei, ya gode wa al’ummar Iran da Iraki saboda gagarumar rawar da suka taka a jana’iza da

Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatollah Seyyed Mojtaba Khamenei, ya gode wa al’ummar Iran da Iraki saboda gagarumar rawar da suka taka a jana’iza da kuma tarurukan ban kwana ga Shahid Ayatollah Seyyed Ali Khamenei.

Ayatollah Seyyed Mojtaba Khamenei, babban dan jagoran, ya isar da wannan sakon ne a ranar Talata yayin wani bikin tunawa da tsohon jagoran a Tehran.

A cikin sakon nasa, Ayatollah Seyyed Mostafa Khamenei ya yi ta’aziyya ga al’ummar Musulunci, al’ummar Iran, inda ya bayyana wannan rashin a matsayin “babban bala’i” da ke bukatar hakuri.

An binne Shahid Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ne da sanyin safiyar ranar Juma’ar data gabata a birnin Mashad bayan kwanaki biyar na tarurukan jana’iza a Tehran, Qom da Iraki, inda miliyoyin mutane suka yi ban kwanan karshe ga Ayatollah Seyyed Ali Khamenei.

Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya yi shahada ne a ranar 28 ga Fabrairu, tare da wasu iyalansa hudu da manyan jami’an soja, a wani harin sama da Amurka da Isra’ila suka kai kan ofishinsa da ke tsakiyar Tehran.

Seyyed Ali Khamenei ya jagoranci Iran daga watan Yunin 1989, bayan rasuwar wanda ya kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Imam Khomeini.

A halin yanzu dan sa Ayatollah Seyyed Mostafa Khamenei, ne ke jagorantar Iran a matsayin jagoran na uku.

Shi ma an bayyana cewa ya samu raunuka a yayin hare haren kawancen na Amurka da Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted