Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasser Kanaani ya ce tattaunawar tsagaita bude wuta a zirin Gaza ba ta da alaka da ‘yancin da Iran take da shi na mayar da martani kan kisan da aka yi wa Ismail Haniyeh a cikin kasar Iran.
Kanaani ya kara da cewa a wani taron manema labarai, “Dole ne mu raba martanin da Iran kan kisan gillar da Isra’ila ta yi wa Shahid Haniyah da kuma batun tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza.
Ya kara da cewa, “Mun yi kokari matuka wajen ganin an tsagaita bude wuta a Gaza, muna kuma goyon bayan kokarin da kasashe abokkanmu masu shiga tsakani suke yi na ganin an kawo karshen bala’in da ke faruwa a zirin Gaza, don haka muna ganin cewa, wadannan shawarwarin ba su da wata alaka da batun mayar da martani na Iran.”
Ya yi nuni da cewa, “ta hanyar kashe Haniyyah, a tabbatar da cewa yahudawan sahyuniya ba son cimma wata matsaka kan batun dakatar da bude wuta da kuma kawo karshen kisan kiyashin da suke yi a Gaza.
Ya jaddada cewa “Iran ba ta son yaki a yankin, amma dole ne ta mayar da martani a daidai lokacin da ya dace bisa la’akari da gazawar kwamitin sulhu kan wannan batu.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya ci gaba da cewa: Wasu kasashen yammacin duniya sun ki yin Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa shahid Haniyyah, tare da hana fitar da wata sanarwa kan Isra’ila a kwamitin sulhu, don haka muna ganin cewa bukatar rashin mayar da martani bai dace ba, kuma ya saba wa hankali da ma dokokin kasa da kasa.”
Ya kara da cewa, “Muna daukar irin wadannan bukatu a matsayin karfafa gwiwar yahudawan sahyoniya don ci gaba da kai hare-hare da aikata laifukan yaki.”