Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya godewa ministan harkokin wajen kasar Omman

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ila Bagaei ya godeawa ministan harkokin wajen kasar Omman kan yadda ya shirya ya kuma gabatar da tattaunawa tsakanin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ila Bagaei ya godeawa ministan harkokin wajen kasar Omman kan yadda ya shirya ya kuma gabatar da tattaunawa tsakanin JMI da Amurka a birnin Mascat da kuma kai kawon da yayi a  tsakanin bangarorin biyu.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Bagaei yana bayyana haka a wani sakon da ya aika a cikin shafinsa na X  a jiya Asabar, ya kuma aika da sakon ne a dai dai lokacinda ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana kan hanyarsa ta dawowa Tehran, bayan tattaunawar. Ya kuma kara da cewa yana fatan Badr bin Hamad Al Busaidi zai ci gaba da wannan kokarin a ranar Asabar mai zuwa inda bangarorin biyu zasu sake haduwa, sannan har zuwa karshen tattaunawar. Bayan kammala tattaunawar dai,  shugaban tawagar JKI a tattaunawar kuma ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana a shafinsa na X kan cewa, tattaunawar ta yi armashi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments