Wasu kafafen yada labarai a kasar Iraki sun bayyana cewa, jiragen yakin Amurka da Saudia sun kai hare hare a kan wasu yankuna a kasar Iraki wadanda suka hada da Ninawa Karbala da wasu wurare a safiyar yau Laraba.
Majiyar gwamnatin kasar Iraki sun bayyana cewa saudia da Amurka sun kai hare haren ne kan sansanonin dakarun Hashdu shaabi a wurare daban daba a kasar ta Iraki. Kuma ya zuwa yanzun sun kai mutane 5 ga shahada a yayinda wasu da dama suka ji rauni.
Kafin haka dai gwamnatin kasar Saudia ta yi zargin cewa a cilla mata makamai Drones daga kasar Iraki, amma dakarun Hasdu sun musanta hakan.
Tashar talabijan ta Almayadeen ta bada labarin cewa an kai hare hare kan wasu wurare a lardin Ninawa da inda ake zaton akwai dakarun Hashdu Shaabi a cikinsa.