Jiragen yakin Amurka sun kai sabbin hare-hare kan wasu yankunan a kasar Yemen a safiyar a jiya Asabar, wadanda suka Baida Sa’ada da kuma Hudaidah wadanda sune sake zafafa yaki a ciki kasar na baya-bayan nan.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labarai na kasar ta Yemen na fadar cewa jiragen yakin kasar ta Amurka sun kai hare-hare har 5 a kan makarantar koyon sana’o’ii na Al-sawma da ke lardin Al-Bayda a jiya Asabar .
Labarin ya kara da cewa makarantar ita ce babbar makaranta a yankin, kuma cibiyar ilmi mafi girma. Har’ila yau labarin ya bayyana cewa jiragen yakin kasar ta Am,urka sun kai hare-hare har guda 3 a kan garin Al-Sahleen daga cikin yankunan Kitif da kuma Al-Bogee daga cikin lardin Sa’ada.
Labarin ya kara da cewa wannan yankin yana daga cikin yankunan da ake fafatawa da sojojin Amurka, kuma suna yawaita kan hare-hare a cikinsa.