Jakadan Amurka A Tel Aviv Ya Ce “Isra’ila” Tana Da Hakkin Mamaye Dukkanin Kasashen Yammacin Asiya

Jakadan Amurka a Tel Aviv  Mike Huckabee ya bayyana cewa; Abu ne da zai zama karbabbe, idan har Isra’ila ta shimfida ikonta akan gabas ta

Jakadan Amurka a Tel Aviv  Mike Huckabee ya bayyana cewa; Abu ne da zai zama karbabbe, idan har Isra’ila ta shimfida ikonta akan gabas ta tsakiya baki daya, yana mai dogaro da nassi na Attaura.

A cikin hirar da Tucker Carson ya yi da jakadan na Amurka a Tel Aviv ya ce: Tsohon alkawali Ubangiji ya yi wa Annabi Ibrahim alkawalin wani yanki na kasa, wanda ya tashi daga Kwarin kasar Masar, zuwa tafkin “Furat”. Wannan kuma yanki ne mai girma wanda ya hade mafi yawancin gabas ta tsakiya, da ya kunshi Jordan, Syria,Lebanon, da kuma wasu sashe na Saudiyya da Iraki.

Haka nan kuma jakadan na Amurka a Tel Aviv ya ce; “Isra’ila” wani yanki ne da Ubangiji ya bai wa zababbiyar al’umma” da hakan yake a matsayin Ishara da nassin da ya zo a cikin littatafan yahudawa.

A lokacin da dan jarida Carson  ya tambayi jakadan na Amurka a “Isra’ila” ko abinda yake nufi shi ne hakkin Isra’ila na shimfida ikonta akan yanki mai yawa na kasa, sai ya amsa da cewa; Zai zama karbabben abu idan  har ta shimfida ikonta a cikin yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted