Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Makiya Suna Hasadan Ci Gaban Kasar Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Makiya suna cike da takaici da fushi kan ci gaban da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take samu

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Makiya suna cike da takaici da fushi kan ci gaban da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take samu

A yayin ganawarsa da manyan kwamandojin sojojin kasar Iran a yau Lahadi, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa; Ci gaban da Iran ta samu ya fusata da kuma kara takaicin masu mugun nufi kan lasar ta Iran. Yana mai bayyana cewa, tabbas akwai rauni a fannonin da suka shafi tattalin arziki da ya kamata a magance.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi la’akari da cewa; Sojojin kasar suna matsayin kariya ta al’umma da kuma mafakar al’umma daga duk wani mai wuce gona da iri, sannan kuma ya jaddada wajibcin ci gaba da bunkasa shirye-shirye da kayan aiki da tsare-tsare don sauke wannan nauyi na kasa. Ya kara da cewa: Ci gaban da kasar ta samu ya fusata da kuma kara takaicin masu adawa da Iran, kuma ko shakka babu akwai raunin da ya faru a fannonin da suka shafi tattalin arziki da babu shakka akwai bukatar a magance shi. Jagoran ya bayyana shirye-shiryen kayan aikin sojojin a matsayin ma’ana inganta karfin makamansu da inganta tsarin su da kuma yadda suke rayuwa. Ya kara da cewa, “Bugu da ƙari, shirye-shiryen kayan aiki, shirye-shirye ne na gudanar da tsare-tsare – wato imani da manufa da sako da kuma tabbatar da halaccin hanyar – wadanda suke da matukar muhimmanci, kuma akwai ƙoƙari na makiya na neman murguda su.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments