gwamnatin yahudawan sahyuniya ta aike da sakon gargadi kai tsaye ga Kasar Labanon cewa za ta kai mummunan hari a muhimman wurare a kasar kamar filin hawa da saukar jiragen sama na birnin Berut, idan kungiyar Hizbullah ta shiga yakin Iran da Amurka,
wasu manyan jami’an kasar labanon guda biyu sun bayyana a jiya talata cewa sakon ya iso ne ta hanyar diflomsiyya inda isra’ila ta bayyana cewa zata yi raga raga da muhimman wuraren a kasar labanon inda kungiyar huzbullah ta taimakawa Iran a yakin da za’ayi tsakaninta Amurka
wannan gargadin yana zuwa ne adaidai lokacin da Tehran da Washington za su fara tattaunawa zagaye na 3 a ranar 26 ga watan fabareru a janeva, kamar yadda ministan harkokin wajen kasar Yamen Sayyid badr bin Hamad albusaidi ya sanar adaidai lokacin da ake cikin yanayi na fargabar barkewar yakin soji tsakanin bangarorin biyu.
sakatare janar din kungiyar Hizbullah Naim Qaseem ya bayyana cewa ba za su zuba ido ba, idan yaki ya barke tsakanin kasar Amurka da jamhuriyar Musulunci ta iran, mun sha alwashen kare kanmu, kuma zamu zbi yadda zamu yi aiki nan ba da jimawa ba.