Isra’ila na ci gaba da kai hare hare a kudancin Lebanon wanda ya fuskanci sabbin hare-haren sama na Isra’ila duk da tsagaita wuta.
Hare haren sun shafi garuruwa da kauyuka da dama, inda ka samu hasarar rayukan mutane sama da 100 a baya baya nan da haifar da kaurar jama’a da dama a yankin.
A cewar hukumomin Lebanon, adadin wadanda suka mutu ya zarce 2,600.
A safiyar ranar 4 ga Mayu, jiragen saman Isra’ila sun ci gaba da kai hari kan garuruwan kan iyaka, don haka suna ci gaba da kai hari a Kudancin Lebanon.
A ranar 3 ga Mayu, sojojin Isra’ila sun ba da umarnin ficewa daga kauyuka goma sha daya a Kudancin Lebanon.
A halin yanzu, Hezbollah ta dauki alhakin kai hare-haren jiragen sama marasa matuka da dama kan wuraren Isra’ila a kudancin Lebanon a matsain maid amartani kan ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta daga Isra’ila.