Sojojin Isra’ila sun kashe Falasɗinawa aƙalla 17, waɗanda suka haɗa da fiye da ƙananan yara 10, sannan suka jikkata gommai a hare-haren da suka kai gidaje biyu a Birnin Gaza da Rafah.
A sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Nuseirat, sojojin Isra’ila sun kashe Falasɗinawa aƙalla takwas.
Wasu ganau sun ce jiragen yaƙin Isra’ila sun kashe Falasɗinawa 16, ciki har da yara 10, kana suka jikkata mutane da dama a harin da suka kai wani gida a yankin Al-Daraj na Birnin Gaza.
Kazalika, wasu majiyoyi sun ce dakarun Isra’ila sun kashe wani Bafalasɗine yayin da suka kai hari a gidan wani mutum mai suna Al-Sha’er a Rafah da ke kudancin Gaza.
Isra’ila ta kwashe kwana 231 tana kai hare-hare a Gaza abin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 35,709 — galibinsu jarirai da mata da yara — sannan ta jikkata sama da mutum 79,990, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine.