IRGC Ta Sanar Da Kai Wa Jiragen Yakin Amurka Hare-hare

Dakarun kare juyin musulunci na Iran sun sanar da cewa sun kai wa jiragen yakin Amurka hare-hare da kuma wasu jiragen dakon mai wadanda su
tambarin irgc

Dakarun kare juyin musulunci  na Iran sun sanar da cewa sun kai wa jiragen yakin Amurka hare-hare da kuma wasu jiragen dakon mai wadanda su ka keta dokokin wucewa ta mashigar Ruwan Hurmuz.

Sanarwar ta kunshi cewa;

“Ya ku al’ummar jamhuriyar musulunci ta Iran masu Imani, amincin Allah ya tabata a gare ku.

Ta hanyar fitowar da kuke yi a cikin fagagen taruka acikin kasa tsawon kwanaki 190  dare da rana, kun tabbatar da cikakkiyar basira da tsayin daka da jajurcewa.

Toku sani cewa ‘yayanku  na sojojin ruwa  na dakarun kare juyi  masu kishi da suke ci gaba da shimfida ikonsu a mashigar Ruwan Hurmuz, suna kuma ci gaba da aikin da rataya awuyansu na kare al’ummar Iran da amana ce a wuyansu.”

Haka nan kuma bayanin ya ce Dakarun kare juyin na ruwa sun mayar da martani akan sojojin ta’addanci na Amurka saboda harin da su ka kai wa jiragen dakon Ruwan Iran 5 a tekun Pasha. Dakarun na IRGC sun kai hari akan jiragen yakin Amurka guda biyu dakuma wasu jiragen dakon mai 8 da su ka keta dokokin shiga ta mashigar ruwa Hurmuz da hakan ya haddasa musu asara mai yawan gaske.

Bayani ya kuma bayyana cewa, jiragen dakon man da aka kai wa hari, sun so ratsawa ne ta wata hanya bisa zugar da Amurka ta yi musu.

A karshe bayanin ya ce, ilahirin mashigar Ruwan Hurmuz tana a karkahsin sa idon IRGC da kuma hukumar da take kula da kai da komowa ta ruwa.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted