Dakarun IRGC na kasar iran sun kai hare hare kan sansanin sojojin Amurka a kasar Jordan tare da amfani da makamai masu linzami samfurin balistic.
Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto majiyar dakarun na fadar haka ta kumakara da cewa ta kuma cilla makamai kan jiragen ruwan daukar ban fetur guda uku wadanda suka yi kokarin wucewa ta mashigar ruwa ta Hurmuz .
Almayadeen ta nakalto majiyar na cewa, matukar sojojin kasar Amurka sun ci gaba da barazana ga amincin kasar Iran gwagwarmaya da su ba zai kare ba. Yakuma kara da cewa dakarun IRGC sun ci gaba da kai hare hare kan sansanin sojojin Amurka da suke Jordan, don tabbatar da cewa Amurka ta daina shishigi cikin al-amuran kasar.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto labarin da ke cewa an ji karar tashin boma bomai a wasu wurare a cikin kasar Jordan.
Kafin haka dakarun na IRGC sun rika sun gargadi mutanen da suke zaune kusa da sansanonin sojojin Amurka a kasashen larabawa na yankin su nisanci wuraren, don kada makaman dakarun su same su.