Dakarun kare juyin musulunci na Iran sun sanar da cewa; Rundunarta ta ruwa tana ci gaba da shimfida ikonta akan mashigar ruwan Humuz, kuma duk wani yunkuri na kasashen wajen yankin na tsoma baki, to zai fuskanci mayar da martani mai tsanani.
Bayanin ya kuma ce; wasu jiragen ruwa biyu na dakon man fetur sun yi kokarin wucewa ta wata hanya daban wacce ba ta da aminci a kudancin mashigar ruwa Hurmuz,da hakan ya haddasa tashin gobara a cikinsu don haka su ja da baya zuwa inda su ka fito.
Bayanin ya ci gaba da cewa; Duk wani yunkuri daga waje na tsoma baki a mashigar ruwan ta Hurmuz, to zai fuskanci mayar da martani mai tsanani.
A wani labarin mai alaka da Hurmuz, jirgin ruwan kasar Qatar na dakon gas, ya wuce ta hanyar da Iran ta ayyana bayan tsaikon da aka samu na tsawon makwanni uku.
Kamfanin dillancin labarun “Tasnim” na Iran ya nakalto cewa;A baya an sami tsaikon kai da komowar jiragen ruwa acikin mashigar ruwan ta Hurmuz, saboda yadda Amurka ta keta yarjejeniyar fahimtar juna.
Jirgin ruwan na Kasar Qatar ya wuce ne bayan da ya tuntubi Iran ba tare da wata matsala ba.