Dakarun sa-kai na Iraki _Hashdus-sha’abi-sun sanar da cewa adadin wadanda su ka yi shahada sanadiyyar harin hadin gwiwa na Amurka da Saudiyya ya kai 20.
Sanarwar ta kuma ce, baya ga wannan adadin na shahidai da akwai kuma wasu mutane 30 da su ka jikkata. Hare-haren na Saudiyya sun shafi gundumomin Bagadad, Wasit, Nenava, Basra da Karkuku. Sai kuma Karbala da Dayali.
Baya ga asara ta rayuka hare-haren sun kuma lalata gine-gine da motocin soja masu yawa.
Sai dai kuma sanarwar ta ce har yanzu ana ci gaba da kididdga barnar da hare-haren na Saudiyya da Amurka su ka kai, ba a kai ga kammalawa ba.
Kungiyoyin gwagwarmayar na Iraqi sun karyata cewa sun kai wa Saudiyya hari. Haka nan kuma sun zargi Saudiyyar da cewa saboda ta gajiya ne a gaban kasar Yemen, take neman karkatacciyar kukar da za ta hau.
Bugu da kari,kungiyoyin sun ce, tabbas Saudiyya za ta fuskanci mayar da martani da zai sa mu yin nadama.