Iran Tana Shirin Gudanar Da Gangamin Ranar Qudus Ta Duniya Karo Na 46

A dai dai lokacinda al-amarin Falasdinawa ta zama babban al-amari a fagen kasa da kasa a duniya, jami’an gwamnatin JMI sun bada sanarwan gudanar da

A dai dai lokacinda al-amarin Falasdinawa ta zama babban al-amari a fagen kasa da kasa a duniya, jami’an gwamnatin JMI sun bada sanarwan gudanar da gangami ko jerin gwanon ranar Qudus ta duniya karo na 46.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu shirya jerin gwano na ranar Qudus ta duniya sun ce a halin yanzu matsalar Falasdinawa wadanda aka mamaye kasarsu shekaru kimani 80 da suka gabata, ta ketare kasashen musulmi da asia ta kuma zama matsala ta farko a duniya.

Labarin ya kara da cewa, wannan yana faruwa duk tare da cewa HKI da kawayenta a kasashen yamma sun yi iya abinda zasu yi na hana yaduwar al-amarin. Sai dai ta kasa yin hakan.

Shugaban ‘Intifadah da Qudus’ a nan irin yace a wannan shekara ma, al-amarin falasdinawa shi ne mafi muhimmancin al-amura ga mutane a duniya, duk tare da kissan falasdinawa fiye da 72,000 a Gaza.

Imam Khomaini (q) wanda ya jagoranci samar da JMI bayan nasarar da ya samu na kifar da gwamnatin Pahlawi a nan kasar Iran a shekara 1979, ya sanya ranar Jumma’a ta karshe na ko wani watan Ramadan ya zama ranar Qudus ta duniya. Ya kuma yi kira ga musulmi a ko ina suke a duniya su raya wannan ranar don farkar da duniya kan al-amarin Falasdinawa.

A halin da ake ci ki dai yahudawan Sahyoniyya suna ci gaba da kashe Falasdina a kasarsu, suna kwace filata suna gonawa ko rusa gidajensu da kuma korarsu daga kasarsu. Musulmi da wadanda ba musulmi ba a fadin duniya suna raya wannan rana ta Qudus don ci gaba da raya al-amarin falasdinawa a duniya har zuwa ranar da zasu sami yanci da kuma dawo da kasarsu daga hannun wadanda suka mamayeta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted