Iran Ta Yi Tir Da Harin Amurka Da Saudiyya Kan Iraki

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah Wadai da hare-haren wuce gona da iri da Amurka da Saudiyya suka kai a yankuna da dama a

Harin Amurka da Saudiyya a Iraki

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah Wadai da hare-haren wuce gona da iri da Amurka da Saudiyya suka kai a yankuna da dama a Iraki.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar Harkokin Wajen ta yi Allah Wadai da hare-haren Amurka da Saudiyya, wadanda suka kai kan yankuna da dama a Iraki, ciki har da wuraren da ke karkashin hukumomin Iraki da kuma jerin gwanon tattakin Arbaeen.

Ma’aikatar ta bayyana hare-haren a matsayin “wani hari a fili kan ikon mallakar kasa da kuma cikakken yankin Iraki da kuma keta Sashe na 4 na Sashe na 2 na Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da kuma muhimman dokokin kasa da kasa.”

Ta kara da cewa an kai hare-haren ne “bisa ga burin Amurka da gwamnatin Sahayoniya na fadada yaki da rikici a yankin Yammacin Asiya.”

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta kuma isar da ta’aziyyarta kan shahadar wasu ‘yan kasar Iraki a hare-haren tare da sake jaddada “cikakkiyar goyon baya da hadin kai da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke yi wa gwamnati da al’ummar Iraki.”

Ta kara da cewa “gwamnatin Amurka ce ke da alhakin mummunan sakamakon wadannan munanan ayyuka, da kuma tayar da hankali.”

Bayanai daga Iraki sun ce akalla mutum 20 ne sukayi shahada kana wasu 32 sun ji rauni a hare-haren hadin gwiwa da Saudiyya da Amurka suka kai a fadin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted