Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta musanta zargin da Amurka ta yi ma ta na hadin guiwar soji da Yemen da kuma Ansarullah.
Amir Said Iravani, jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya, a wata wasika da ya aike wa shugaban kwamitin sulhu da babban sakataren MDD, ya yi watsi da zargin da Amurka ke yi ma Iran na hadin gwiwar soja da Yemen da Ansarallah.
A cikin wasikar : Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake yin watsi da wadannan zarge-zarge data danganta da marasa tushe.
Iran dai na daukar irin wadannan tuhume-tuhumen a matsayin wani bangare na ajandar siyasar Amurka, wanda manufarsa ita ce yin rufa-rufa da halasta ayyukan wuce gona da iri da kasar ke yi a halin yanzu na nuna adawa da ‘yancin kan kasar Yemen.
Haka kuma, a yanzu ya fito fili fiye da kowane lokaci cewa Amurka na neman tursasa kwararrun Majalisar Dinkin Duniya da su sabawa yanci da nauyin da ya rataya a yuwansu.
“Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana karara a lokuta da dama, ciki har da a cikin wasikar, cewa ba ta da hannu cikin ayyukan da suka saba wa kudurin kwamitin sulhun.
Don haka manufofin Iran game da rikicin kasar Yemen a bayyane yake,”
“Iran na goyon bayan warware rikicin Yemen cikin lumana da kuma hanyar diflomasiyya tare da jaddada kudirinta na tabbatar da tsaron teku da ‘yancin zirga-zirga.
Duk da haka, gaskiyar magana ita ce, Amurka da kawayenta suna da alhakin keta dokokin kasa da kasa, Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya da kudurorin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ta hanyar cin zarafi ga ‘yancin kai da yankin Yemen,” in ji jami’in diflomasiyyar.