Iran: Killace Mashigar Hormuz Yana Nufin Faɗaɗa Matakin Yaƙi Ne

Hedikwatar Rundunar Sojin Khatamal- Anbiya ta Iran ta jaddada cewa: Killace yankin mashigar Ruwan Hormuz yana nufin faɗaɗa matakin yaƙi ne Hedikwatar Rundunar Sojin Khatamal-Anbiya

Hedikwatar Rundunar Sojin Khatamal- Anbiya ta Iran ta jaddada cewa: Killace yankin mashigar Ruwan Hormuz yana nufin faɗaɗa matakin yaƙi ne

Hedikwatar Rundunar Sojin Khatamal-Anbiya (Alaihissalam) ta fitar da wata sanarwa a ranar Litinin tana nuni da cewa: Ci gaba da munanan ayyukan Amurka, musamman ayyukanta na kawo cikas a yankin, da kuma sanya takunkumin jiragen ruwa ba bisa ka’ida ba a kan Iran a cikin ‘yan kwanakin nan. Sanarwar ta yi gargadin cewa wannan matakin na Amurka yana nufin kara kaimin rikici ne a yankin.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: A wani mataki na rashin imani da rashin tsaro a yankin, da kuma bayan sanya takunkumin jiragen ruwa ba bisa ka’ida ba a kan Iran, Amurka ta yi barazana ga jiragen ruwan kasuwanci na Iran da jiragen ruwan mai a cikin ruwan gabar teku da na yankuna a cikin kwanaki uku da suka gabata.

Sanarwar ta kamala da cewa: “Iran tana gargadin cewa wannan matakin na Amurka ya nuna karuwar rikici a yankin. Kamar yadda rundunar sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa, ba za ta lamunci duk wata barazana ko tsokana daga sojojin Amurka ‘yan ta’adda ba kuma za ta mayar da martanin da ta dace.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted